1.0 KiB
1.0 KiB
sanda, sanduna
Ma'ana
kalmar "sanda" wani itace ce miƙaƙƙe mai kauri da ake amfani da shii ta hanyoyi daban-daban. Ta kai kamar mita ɗaya a tsayi.
- Makiyaya na amfani da sandar itace don tsare garke daga wasu dabbobin. Ana kuma jefa ta ga tunkiyar da ta bijire domin a maido cikin garken.
- A Zabura 23, sarki Dauda ya yi amfani da kalmomin "sanda" da "kere" domin ya nuna bishewar Allah da kuma horarwarsa ga mutanensa.
- Sandar makiyayi akan yi amfani da ita wajen kirgen tumaki yayin da suke wucewa daga ƙarƙashin ta.
- Akan ce da ita "sandar ƙarfe," ma'ana, Allah na horar da mutane masu tawaye da shi suna kuma aikata mugunta.
- A zamanin dã, sandar ma'auni na ƙarfe, itace, ko dutse akan yi amfani da su a gwada tsawon gini ko wani abu.
- A Littafi Mai Tsarki, sandar itace ana ce da ita kayan aiki na horon yara.
(Hakanan duba: kere, tumaki, makiyayi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Korintiyawa 04:21
- 1 Sama'ila 14:43-44
- Ayyukan Manzanni 16:23
- Fitowa 27:9-10
- Wahayin Yahaya 11:01