723 B
723 B
a bada rahoto, rahontanai, an bada rahoto,
Ma'ana
Kalmar "rahoto" na manufar a faɗi wa mutane game da wani abin da ya faru, yawancin lokuta ana bada bayanin abin da ya faru. Rahoto abin da ake faɗi ne ana kuma iya rubutawa.
- "Rahoto" na iya zama "faɗi" ko "yi bayani" ko "faɗi a dalla-dalla."
- Faɗin nan "kada ka faɗi wa kowa wannan rahoto" ana iya cewa "kada ka yi magana da wani game da wannan" ko "kada ka gaya wa kowa game da wannan."
- Haka kuma, ana fassara "rahoto" kamar "yin bayani" ko "bada labari" ko "bada kasafi," dukka ya danganta da yadda yanayin zancen yake.
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 05:22-23
- Yahaya 12:38
- Luka 05:15
- Luka 08:34
- Matiyu 28:15