1.3 KiB
1.3 KiB
watsi, watsarwa, ƙi, ƙin karɓuwa
Ma'ana
A yi "watsi" da wani ko wani abu na nufin rashin amincewa da wannan mutum ko wani abun.
- Kalmar "watsi" kuma na iya zama "rashin yarda da" wani abu.
- A yi watsi da Allah na nufin a ƙi amincewa da shi.
- Lokacin da Isra'ilawa suka ƙi shugabancin Musa, ya nuna da cewa suna tawaye ne ga ikonsa. Basu so ne su yi biyayya da shi.
- Isra'ilawa sun nuna cewa sun yi watsi da Allah a sa'ad da suka yi sujada ga allolin ƙarya.
- Kalmar "tũrewa" shi ne ainihin ma'anar wannan kalma. Wasu yarurruka za su iya samun irin wannan da ke ma'anar watsi ko ƙin a gaskata da wani ko wani abu.
Shawarwarin Fassara:
- Ya danganta da nassin, kalmar "watsi" za a iya fassarawa haka "a ƙi karɓa" ko a "daina taimako" ko "a ƙi yin biyayya" ko "a daina yin biyayya."
- A faɗar "dutsen da magina suka watsar," kalmar "watsi" za a iya fassarawa "a ƙi amfani da" ko "a ƙi karɓa" ko "a yar" ko "a kawar a matsayin marar amfani."
- A nassin da mutane suka yi watsi da dokokin Allah, za a iya fassara watsi haka "ƙin yin biyayya" da dokokinsa ko "an zaɓi a taurare daga karɓar" shari'ar Allah.
(Hakanan duba: doka, rashin biyayya, biyayya, taurin wuya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Galatiyawa 04:12-14
- Hosiya 04:6-7
- Ishaya 41:09
- Yahaya 12:48-50
- Markus 07:09