884 B
884 B
tsautawa,
Ma'ana
A tsauta na nufin a yi wa wani kasheɗi mai ƙarfi da murya, yawancin lokuta domin a juyo da shi daga zunubi. Wannan kasheɗin tsautawa ne.
- Sabon Alƙawari na umartar Kiristoci su tsautawa wasu masu bin sa'ad da suke tafiya a zahiri cikin rashin biyayya ga Allah.
- Littafin Misalai ya umarce iyaye da su tsautawa 'ya'yansu lokacin da suke rashin biyayya.
- Tsautawa ana yin ta ne don a kiyaye waɗanda suka aikata laifi kada su ƙara dulmaya kansu cikin zunubi.
- Ana iya fassara ta da nufin "kasheɗi mai ƙarfi" ko "faɗakarwa."
- Ana iya faɗin kalmar "ɗan tsautawa" a ce "kasheɗi mai ƙarfi" ko "gyara mai ƙarfi."
- "Rashin tsautawa" ana iya fassara shi "rashin shawara" ko "rashin gyara."
(Hakanan duba: shawara, rashin biyayya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Markus 01:23-26
- Markus 16:14
- Matiyu 08:26-27
- Matiyu 17:17-18