2.1 KiB
2.1 KiB
tada, kiwata, tada, tashi, tashi, taso, tashi, zuga sama
Ma'ana
tashi, tashi tsaye
A taƙaice kalmar "tada" na manufar " ɗaga sama" ko "a sa a yi sama."
- Kalmar jimlar "tada sama" na ma'anar a ingiza wani abu ya bayyana ko kasance. Yana iya zama kuma a sanya wani a matsayin yin wani abu.
- Wani lokacin "tada sama" na iya nufin "maidowa" ko "sãke ginawa."
- "Tadawa" na da ma'ana ta musamman "tayarwa daga matattu." Ma'ana a tada mataccen mutum domin ya rayu.
- Wani lokacin "tada sama" na manufar " a girmama" wani ko wani abu.
tashi, a tashi
"Tashi" ko "a tashi" na ma'anar "a yi sama" ko "a haura sama." Kalmomin "an tashi," "an taso" da "tasowa" suna bayyana abin da aka riga aka yi.
- Idan wani taliki ya tashi za shi wani wuri, wannan wani lokaci ana bayyana shi a "ya taso ya tafi" ko "ya tashi ya tafi."
- Idan wani abu ya "taso" ana nufin "kasance" ko "ya fara kasance wa."
- Yesu ya faɗi cewa zai "tashi daga matattu." Kwanaki uku bayan Yesu ya tashi, mala'ikan ya ce, "Ya tashi!"
Shawarwarin Fassara:
- Kalmar "tashi" ko "tasowa sama" ana iya fassarawa "ɗagawa sama" ko "a sa ya yi bisa."
- "Tasowa sama" ana kuma iya fassarawa "a sa ya bayyana" ko "a ƙayyada" ko "a kawo zuwa wanzuwa."
- "Tasowar da ikon maƙiyanka" za a iya fassarawa haka, "sanya maƙiyanka su zama da ƙarfi sosai."
- Faɗar "tada wani daga matattu" ana iya fassarawa haka "a sanya wani ya dawo daga mutuwa zuwa rai" ko "sanya wani ya dawo zuwa rai."
- Ya danganta ga nassin, "tasowa sama" za a iya fassarawa haka "a wadata" ko "a ƙayyada" ko "a sa a samu" ko "a gina" ko "a sake ginawa" ko "a yi gyara."
- faɗar "ya taso ya tafi" za a iya fassarawa haka "ya tashi ya tafi" ko "ya tafi."
- Ya danganta ga nassin, kalmar "ya taso" za a iya kuma fassarawa haka "farawa" ko "a fara yin" ko "a tashi tsaye" ko " a tsaya tsaye."
(Hakanan duba: tashi daga matattu, ɗaukaka)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 2 Tarihi 06:41
- 2 Sama'ila 07:12
- Ayyukan Manzanni 10:40
- Kolosiyawa 03:01
- Maimaitawar Shari'a 13: 1-3
- Irmiya 06:01
- Littafin Alƙalai 02:18
- Luka 07:22
- Matiyu 20:19