1.1 KiB
1.1 KiB
cancanta, cin jarabawa, rashin cancanta, faɗuwa jarabawa
Ma'ana
Wannan magana "cin jarabawa" ana nufin samun 'yancin karɓar tagomashi ko samun karɓuwa cewa wani yana da wata baiwar iyawa.
- Mutumin da ya "ci jarabawa" domin wani aiki na musamman dole yana da baiwa da koyarwar da zai yi wannan aiki.
- A cikin wasiƙarsa zuwa ga iklisiyar Kolosiya, manzo Bulus ya rubuta cewa Allah yaba masu bada gaskiya "yardar ci" su sami rabo a cikin mulkinsa na haske. Manufar wannan shi ne Allah ya basu dukkan abin da suke buƙata suyi rayuwa irin tasa.
- Mai bada gaskiya ba zai yi aiki domin ya sami 'yancin zama mai rabo a mulkin Allah ba. Ya ci jarabawa domin Allah ya fanshe shi ta wurin jinin Yesu.
Shawarwarin Fassara:
- Ya danganta ga nassi, "cancanta" za a iya fassarawa haka "shiryayye" ko "mai hattara" ko "samun iyawa."
- Idan an sa mutum ya "ci jarabawa" za a iya fassarawa haka "an shirya shi" ko "an ba shi iyawa" ko "an ƙarfafa masa gwiwa."
(Hakanan duba: Kolosse, allantaka, mulki, haske, Bulus, fansa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Daniyel 01:3-5