703 B
703 B
kumbura, cika da batsewa
Ma'ana
Wannan magana "kumbura" furci ne da aka misalta mutumin dake da girman kai ko fahariya.
- Mutum mai kumburi yana da halin ganin yafi waɗansu.
- Bulus ya koyar cewa sanin abubuwa da yawa ko istiharan addini zai iya sa kumburi ko girman kai.
- Wasu yarurruka watakila suna da magana irin haka ko wani daban daya bayyana wannan ma'ana, kamar a ce "'yana da ƙaton kai."
- Za a iya kuma fassarawa haka "mai girman kai ainun" ko "'wanda yake rena mutane" ko "hura hanci" ko "tunanin ya fi wasu."
(Hakanan duba: fahariya, girman kai)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Korintiyawa 04:6-7
- 1 Korintiyawa 08:01
- 2 Korintiyawa 12:6-7
- Habakuk 02:04