944 B
944 B
lardi, larduna, gunduma
Ma'ana
Lardi wani yanki ne ko sashen wata al'umma ko mulki. Wannan magana "na lardin" ana nufin abin nan dake game da wannan lardin, misali "gwamnan lardi."
- Ga misali, tsofuwar daular Fasiya an rarraba ta lardi lardi kamar su Mediya, Fasiya Siriya, da Masar.
- A lokacin Sabon Alƙawari, an rarraba mulkin Roma cikin larduna kamar su Makidoniya, Asiya, Siriya,Yudiya, Samariya, Galili, da Galatiyawa.
- Kowanne lardi nada mai ikon mulkinsa, wanda ke ƙarƙashin sarki ko mai mulkin sarautar baki ɗaya. Wannan mai mulki wani lokaci ana ce da shi "hakimin lardi" ko "gwamnan lardi."
- Wannan magana "lardi" da "na lardin" za a iya fassara shi haka "yanki" da "na yankin."
(Hakanan duba: Asiya, Masar, Esta, Galatiya, Galili, Yudiya, Macidoniya, Medes, Roma, Samariya, Siriya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 19:30
- Daniyel 03:02
- Daniyel 06:02
- Littafin Mai Wa'azi 02:08