827 B
827 B
misali, misalai, karin magana
Ma'ana
Karin magana wata guntuwar magana ce wadda ke faɗin wasu hikima ko gaskiya.
- Karin Magana na da ƙarfi domin tana da sauƙin tunawa da kuma maimaitawa.
- Yawancin lokaci karin magana na bada aikatattun misalai ne daga rayuwar yau da kullum.
- Wasu misalan masu sauƙin fahimta ne miƙaƙƙu, wasu kuwa suna da wuyar ganewa.
- Sarki Suleman sananne ne wajen hikimarsa kuma ya rubuta karin magana sama da 1,000.
- Yawancin lokaci Yesu ya yi amfani da karin magana ko misalai sa'ad da yake koyar da mutane.
- Hanyoyin fassara "karin magana" zai haɗa da "faɗin hikima" ko "maganar gaskiya."
(Hakanan duba: Suleman, gaskiya, hikima)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Sarakuna 04:32-34
- 1 Sama'ila 24:12-13
- 2 Bitrus 02:22
- Luka 04:24
- Littafin Misalai 01:1-3