1.2 KiB
1.2 KiB
rusunawa, sujada, faɗuwa ƙasa rub da ciki
Ma'ana
Wannan magana "rusunawa" na nufin kwanciya da fuska ƙasa, a miƙe a ƙasa.
- "A faɗi a rusuna" a gaban wani shi ne a sunkuya nan da nan ƙasa sosai a gaban wani mutum.
- Yawancin lokaci ana rusunawa saboda tsorata ne, mamaki, da bangirma, saboda wani abin al'ajibi ya faru. Yana kuma nuna girmamawa da darajanta mutumin da aka sunkuya wa.
- Rusunawa wata hanya ce ta yiwa Allah sujada.
Yawancin lokaci mutane suna yiwa Yesu haka domin godiya da sujada lokacin da ya yi abin al'ajibi ko domin su girmama shi a matsayin babban malami.
- Ya danganta ga nassi, wasu hanyoyin fassara "rusunawa" za a haɗa da waɗannan, "sunkuyawa ƙasa da fuska har ƙasa" ko "yi masa sujada ta wurin kwanciya da fuska ƙasa a gabansa" ko "sunkuyawa ƙasa don mamaki" ko "sujada."
- Wannan furci "ba zamu rusuna kanmu ba" za a iya fassarawa haka, "ba za muyi sujada ba" ko "ba zamu kwanta da fuskoki ƙasa muyi sujada ba" ko "ba zamu rusuna mu yi sujada ba."
- "Ya rusuna wa" za a iya fassara wannan haka, "yin sujada" ko 'sunkuyawa a gabansa."
(Hakanan duba: jin tsoro da girmamawa, sunkuyawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 2 Sarakuna 17:36-38
- Farawa 43:28
- Wahayin Yahaya19:3-4