ha_tw/bible/other/profane.md

884 B
Raw Permalink Blame History

ƙazantar, ƙazantacce, ƙazantarwa

Ma'ana

Idan an ƙazantar da wani abu an gurɓanta shi ko an ɓata shi, ko a tozartar da wani abu mai tsarki.

  • Ƙazamin mutum shi ne wanda yake yin abubuwa marasa tsarki yana ƙasƙantar da Allah.
  • Wannan magana "ƙazantarwa" za a iya fassarawa haka, "a ɗauki abu ba tsarki" ko "a nuna rashin bangirma ga" ko "a yi watsi da."
  • Allah ya cewa Isra'ilawa sun "ƙazantar" da kansu da gumaku, ma'ana, mutanen sun kawo wa kansu "rashin tsarki" ko "ƙasƙanci" ta wurin wannan zunubi. Suna kuma aikata rashin girmama Allah.
  • Ya danganta ga nassi, za a iya fassara "ƙazantarwa" haka "rashin girmamawa" ko "babu tsoron Allah" ko "marar tsarki."

(Hakanan duba: ƙazantu, tsarki, tsabta)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Timoti 02:16-18
  • Ezekiyel 20:09
  • Malakai 01:10-12
  • Matiyu 12:05
  • Littafin Lissafi 18:30-32