709 B
709 B
sokewa, suka, soki, hudawa
Ma'ana
Wannan magana "sokewa" ma'anarta shi ne a tsire wani abu da wani abu mai tsini. Akan yi amfani da ita a misalta yadda ake sa wani mutum ya ji ciwo a ransa.
- Wani soja ya soki kwiɓin Yesu lokacin da aka rataye shi akan gicciye.
- A lokacin Littafi Mai Tsarki, bawan da aka baratar akan huda kunnensa, alamar ya zaɓa ya ci gaba da aiki da maigidansa.
- Simiyon ya yi magana da misali sa'ad da yace wa Maryamu takobi zai soki zuciyarki, ma'ana, zata sami baƙinciki ainun domin abin da zai faru da ɗanta Yesu.
(Hakanan duba: gicciye, Yesu, bawa, Simiyon)
Wuraren da ake samunsa a ittafi Mai Tsarki:
- Ayuba 16:13
- Ayuba 20:23-25
- Yahaya 19:37
- Zabura 022:16