911 B
911 B
baikon salama, baye-baye na salama
Ma'ana
"Baikon salama" ɗaya ne daga cikin hadayun baye-bayen da Allah ya umarci Isra'ilawa suyi. Wani lokaci ana ce da shi "baiko domin godiya" ko "baiko na zumunta."
- Wannan baiko ya ƙunshi yin hadayar dabbar da bata da lahani, akan yayyafa jinin dabbar akan bagadi, a kuma ƙona kitsen, da kuma sauran gaɓoɓin dabbar dabam.
- Ƙari bisa wannan hadayar akwai baikon waina marar gami da mai gami, wanda za a ɗibiya bisa baikon ƙonawa a ƙona.
- Da firist da mai miƙa hadayar an yardar masu su ci daga cikin abincin da aka miƙa.
- Wannan baiko ya kwatanta zumuncin Allah da mutanensa.
(Hakanan duba: baikon ƙonawa, zumunta, baiko na zumunta, baikon na hatsi, firist, hadaya, gurasa marar gami)
Wuraren da ake samunsa a cikin Littafi Mai Tsarki:
- 1 Sama'ila13:8-10
- Ezekiyel 45:16-17
- Yoshuwa 08:30-32
- Lebitikus 09:3-5
- Littafin Misalai 07:13-15