755 B
755 B
haƙuri, yin abu da haƙuri, rashin haƙuri
Ma'ana
Wannan magana "haƙuri" ma'anarta jurewa cikin matsaloli masu wuya. Yawancin lokaci haƙuri na tare da jira.
- Lokacin da mutane suke haƙuri da wani mutum, ana nufin suna nuna ƙauna ne ga mutumin kuma suna yafe dukkan laifofin da mutumin ya aikata.
- Littafi Mai Tsarki ya koya wa 'ya'yan Allah suyi haƙuri sa'ad da suke fuskantar matsaloli kuma suke haƙurce wa junansu.
- Saboda jinƙansa, Allah yana da haƙuri zuwa ga mutane, koda shi ke masu zunubi ne waɗanda sun cancanci hukunci.
(Hakanan duba: jimiri, gafartawa, naciya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Bitrus 03:20
- 2 Bitrus 03:8-9
- Ibraniyawa 06:11-12
- Matiyu 18:28-29
- Zabura 037:7
- Wahayin Yahaya 02:02