901 B
901 B
tãra, nuna bambanci, wariya
Ma'ana
Wannan magana "tãra" da "nuna bambanci" na nufin son zuciyar wani ya bambanta mutane da nufin wasu sun fi wasu mutane mahimmanci.
- Wannan kusan ɗaya yake a ma'ana da nuna wariya, wato a fi son wasu mutane kan wasu.
- Yawancin lokaci ana yin tãra da bambanta mutane domin sun fi wasu arziki ko domin su sanannune fiye da wasu mutanen.
- Littafi Mai Tsarki ya koya mana kada mu nuna tãra ko bambanci ga mutanen dake da arziki ko matsayi.
- A cikin wasiƙarsa zuwa ga Romawa, Bulus ya koyar cewa Allah yana shar'anta mutane da adalci ba ya nuna tãra.
- Littafin Yakubu ya koyar da cewa ba dai-dai bane a ba wani mutum kujera mafi girma ko a fi kulawa da shi domin shi mai arziki ne.
(Hakanan duba: tagomashi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Maimaitawar Shari'a 01:17
- Malakai 02:09
- Markus 12:13-15
- Matiyu 22:16
- Romawa 02:10-12