885 B
885 B
maƙwabci, maƙwabta, maƙwabtaka, makusanta,
Ma'ana
Wannan furci "maƙwabci" na nufin wani mutum dake zaune kusa. Zai iya zama kuma wani mutum da ake zaune tare da shi ko ƙungiyar mutane.
- Maƙwabci wani mutum ne da za a kare ana masa alheri domin shi ɗaya ne daga cikin iyali.
- A cikin Sabon Alƙawari, a labarin Ba'samariye mai alheri, Yesu ya yi amfani da kalman nan "maƙwabci" ya faɗaɗa ma'anarta har zuwa ga dukkan 'yan adam, har ma da wanda ake ɗauka abokin gãba.
- Idan ya yiwu zai fi kyau a fassara wannan kalmar a sauƙaƙe da kalma ko furci mai ma'ana haka, "mutumin dake zaune kurkusa.
(Hakanan duba: abokin gãba, misali, ƙungiyar mutane, Samariya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 07:26-28
- Afisawa 04:25-27
- Galatiyawa 05:14
- Yakubu 02:08
- Yahaya 09:8-9
- Luka 01:58
- Matiyu 05-43
- Matiyu 19:19
- Matiyu 22:39