ha_tw/bible/other/mourn.md

1.0 KiB
Raw Permalink Blame History

makoki, masu makoki, kuka

Ma'ana

Wannan furci "makoki" manufarsa shi ne nuna baƙinciki yawancin lokaci a mutuwar wani mutum.

  • A cikin al'adu da yawa, makoki ya ƙunshi yin wasu abubuwa a sarari da zai nuna baƙinciki da damuwa.
  • Isra'ilawa da sauran mutane a zamanin dã sukan nuna makokinsu ta wurin kwala ihu da kururuwa. Sukan sa kaya mararsa kintsi da aka yi da tsummokara su kuma baɗa toka a kawunansu.
  • Gwanayen makoki, yawancin lokaci mata ne da ake biyan su, za su saka kururuwa suyi kuka mai zafi daga lokacin mutuwar har bayan an bizne gawar a kabari.
  • Ƙayadadden lokacin makoki kwana bakwai ne, amma zai iya zarcewa har kwana talatin (kamar na Musa da Haruna) ko kwana sabba'in (kamar na Yakubu).
  • Littafi Mai Tsarki ya yi magana da misali akan "makoki" domin zunubi. Ya yi magana akan nuna baƙinciki mai zafi domin zunubi yana kawo wa Allah baƙinciki da kuma mutane.

(Hakanan duba: tsummoki, zunubi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila15:34-35
  • 2 Sama'ila 01:11
  • Farawa 23:02
  • Luka 07:31-32
  • Matiyu 11:17