954 B
954 B
mai ba'a, masu ba'a, ba'a, maganganun ba'a, dariyar ba'a
Ma'ana
Wannan kalma "ba'a," dariyar ba'a, da maganganun wofintarwa duk manufarsu ɗaya a mai da wani mutum abin dariya musamman a cikin mugunta.
- Yin ba'a ya ƙunshi kwaikwayon yadda mutum ke magana ko motsawa da nufin kunyatarwa ko nuna reni.
- Sojojin Romawa suka yiwa Yesu ba'a da reni lokacin da suka sa masa al'kyabba suka yi kamar suna girmama shi kamar sarki.
- Wata ƙungiyar mutane matasa suka yiwa annabi Elisha ba'a da dariya da suka kira shi da wani suna, suka yi dariyar kansa mai saiƙo.
- Wannan kalma "dariyar ba'a" ƙarin bayaninsa shi ne yin ba'a ga wani abin da aka ga ba ya gaskantuwa ko mahimmanci.
- Mai ba'a shi ne mutumin da yake ba'a da reni kullayomi.
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki.
- 2 Bitrus 03:04
- Ayyukan Manzanni 02:12-13
- Galatiyawa 06:6-8
- Farawa 39:13-15
- Luka 22:63-65
- Markus 10:34
- Matiyu 09:23-24
- Matiyu 20:19
- Matiyu 27:29