1.3 KiB
1.3 KiB
hankali, tunarwa, tunawa, abin tunashewa, ra'ayi ɗaya
Ma'ana
Wannan kalma "hankali" na nufin wannan fannin mutum dake tunani yana kuma yin zaɓi.
- Hankalin kowanne mutum shi ne jimilar tunaninsa da hikimarsa.
- "Samun hankali irin na Almasihu" shi ne mutum ya riƙa tunani da aiki irin da wanda Almasihu zai yi. Wato za a yi biyayya ga Allah Uba, a yi biyayya da koyarwar Almasihu, ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.
- "Sauya ra'ayi" shi ne wani ya yi zaɓi daban ko ya bada ra'ayi daban da wanda ya bayar da farko.
Shawarwarin Fassara:
- Wannan kalma "hankali" za a iya fassarawa haka "tunani" ko "la'akari" ko "zato" ko "fahimta."
- Wannan magana "tuna da" za a iya fassara ta haka "tuna" ko "ka yi lura da wannan" ko "ka tabbata ka san wannan."
- Wannan furci "zuciya, rai, da tunani za a iya fassara su haka "abin da ake ji a jiki, abin da ka gaskata, da abin da kake tunani a kai."
- Wannan magana "ya canza tunaninsa ya tafi" za a iya fassarawa haka "ya zaɓi ra'ayi daban ya tafi" ko "duk da haka ya zaɓa" ko "ya sauya ra'ayinsa ya tafi."
- Wannan magana raba hankali" za a iya fassara shi a ce "shakka" ko "ruwan ido" ko "yana da ruɗaɗɗen tunani."
(Hakanan duba: gaskatawa, zuciya, rai)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Luka 10:27
- Markus 06:51-52
- Matiyu 21:29
- Matiyu 22:37
- Yakubu 04:08