770 B
770 B
manzo, manzanni
Ma'ana
Wannan magana "manzo" ma'anasa wani mutum da aka bashi saƙo ya je ya faɗa wa waɗansu.
- A zamanin dã, akan aika manzo daga dagar yaƙi ya je ya gaya wa mutane a cikin birni abin da ya faru.
- Mala'ika wani irin manzo ne musamman wanda Allah ke aika su kai wa mutane saƙonni. Wasu juyi sukan fassara "'mala'ika" "manzo" ne.
- An ce da Yahaya Mai Baftisma manzo ne da ya zo kafin Yesu domin yayi shela Almasihu yana zuwa a shirya mutane su karɓe shi.
- Manzannin Yesu sune masu kai saƙonsa ga mutane labari mai daɗi game da mulkin Allah.
(Hakanan duba: mala'ika, manzanni, Yahaya (mai Baftisma))
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Sarakuna 19:1-3
- 1 Sama'ila 06:21
- 2 Sarakuna 01:1-2
- Luka 07:27
- Matiyu 11:10