877 B
877 B
matsakanci
Ma'ana
Matsakanci mutum ne da ya taimaka wa mutum biyu ko mutane da yawa su sasanta jayayya ko rashin jituwarsu da juna.Yakan taimake su su sulhuntu.
- Domin mutane sun yi zunubi, maƙiyan Allah ne sun cancanci hasalarsa da hukuncinsa. Saboda zunubi, zumuncin tsakanin Allah da mutanensa ya tsinke.
- Yesu shi ne matsakanci tsakanin Allah Uba da mutanensa, yana maida dangartaka ta wurin mutuwarsa wadda ita ce biyan bashin zunubanmu.
Shawarwarin Fassara:
- Ga hanyoyin fassara "matsakanci" za a iya cewa haka "mutum mai tsayawa tsakani" ko "mai sulhu" ko "mutumin dake kawo salama."
- Gwada wannan magana da yadda ake fassara "firist." Zai fi kyau idan an fassara "matsakanci" dabam.
(Hakanan duba: firist, sulhunta)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Timoti 02:05
- Galatiyawa 03:20
- Ibraniyawa 08:06
- Ibraniyawa 12:24
- Luka 12:14