889 B
889 B
sha'awa, zaƙuwa, marmari, muradi
Ma'ana
Sha'awa wani irin son zuciya ne mai ƙarfi, yawancin lokaci na son wani abin zunubi ko lalata. Idan an ji sha'awa shi ne yin sha'awa.
- A cikin Littafi Mai Tsarki, yawancin lokaci idan an yi magana akan "sha'awa" ana nufin kwana da wani ko wata batare da aure ba.
- Wasu lokutta kuma wannan kalma a kan yi misali da ita da manufar bautar gumaku.
- Ya danganta bisa ga nassi, za a iya fassara "sha'awa" haka "marmari marar kyau" ko "marmari mai ƙarfi" ko "marmarin jima'i marar dacewa" ko "muradin jiki mai ƙarfi." ko "marmarin yin zunubi."
- Wannan furci "zuwa ga sha'awa" za a iya fassara ta haka "marmari marar dacewa" ko "yin tunanin lalata na jiki" ko "kwaɗayin jiki na lalata."
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Yahaya 02:16
- 2 Timoti 02:22
- Galatiyawa 05:16
- Galatiyawa 05:19-21
- Farawa 39:7-9
- Matiyu 05:28