828 B
828 B
fara, fari
Ma'ana
Wannan kalma "fãri" na nufin wasu manyan ƙwari ne masu tashi cikin cincirindonsu su yi ɓarnar cinye dukkan ganyaye da suka tarar.
- Fãrin nan manya ne, dogaye da fukafukai, kafafunsu na baya suna basu gwanintar tsalle mai nisa.
- A cikin Tsohon Alƙawari, an yi kwatanci da cincirindon fãri a matsayin hoton mummunar lalatarwa da zai abko wa Isra'ila saboda rashin biyayyarsu.
- Allah ya aiko da fãri suka zama ɗaya daga cikin annobai goma da ya aiko gãba da Masarawa.
- Sabon Alƙawari ya ce ƙwaƙƙwaran abincin Yahaya mai yin baftisma fãri ne sa'ad da yake zaune a jeji.
(Hakanan duba: bawa, Masar, Isra'ila, Yahaya (mai Baftisma))
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 2 Tarihi 06:28
- Maimaitawar Shari'a 28:38-39
- Fitowa 10:3-4
- Markus 01:06
- Littafin Misalai 30:27-28