672 B
672 B
dabbobi
Ma'ana
Wannan kalma "dabbobi" na nufin naman da ake kiwo a gida domin abinci da wasu ayyuka kuma. Wasu dabbobin ana horar da su domin aiki.
- Ire-iren dabbobin sun haɗa da tumaki, shanu, awaki, dawakai, da jakuna.
- A lokacin Littafi Mai Tsarki, ana gwada arzikin mutum da yawan dabbobin da yake da su.
- Ana amfani da dabbobi don su bada abubuwa kamar ulu, madara, mai, kayan gida, da tufafi.
- Wannan kalma za a iya fasarata haka "dabbobin gida."
(Hakanan duba: saniya, sã, jaki, akuya, doki, tukiya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 2 Sarakuna 03:15-17
- Farawa 30:29
- Yoshuwa 01:14-15
- Nehemiya 09:36-37
- Littafin Lissafi 03:41