1.1 KiB
1.1 KiB
mazaunin fitila, mazaunin fitili
Ma'ana
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar "mazaunin fitila" a taƙaice yana nufin wani wuri inda ake ɗora fitila domin ta bada haske ga ɗakin.
- Mazaunin fitila mai sauki fitila ɗaya yake riƙewa kuma ana yinsa da yumɓu, katako ko ƙarfe (kamar su tagulla, azurfa, ko zinariya.)
- A cikin haikalin Yerusalem akwai mazaunin fitila na zinariya musamman wanda ke da rassa bakwai domin riƙe fitilu bakwai.
Shawarwarin Fassara:
- Ana iya fassara wannan kalma a matsayin "ƙafar fitila" ko "abin riƙe fitila" ko "mariƙin fitila."
- Game da mazaunin fitilar haikali, ana iya fassara wannan a matsayin "mazaunin fitila bakwai" ko "ƙafar zinariya tare da fitilu bakwai."
- Kuma zai taimaka wurin fassarawa idan aka haɗa da hotunan mazaunin fitila da mazaunin fitila mai rassa bakwai a shafofin Littafi Mai tsarki dake zancen su.
(Hakanan duba: tagulla, zinariya, haske, azurfa, haikali)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Daniyel 05:5-6
- Fitowa 37:17
- Markus 04:21-23
- Matiyu 05:15-16
- Wahayin Yahaya 01:12-13
- Wahayin Yahaya 01:20