837 B
837 B
aiki, aikace-aikace, aikin ƙarfi, ma'aikaci, ma'aikata, aiki tuƙuru
Ma'ana
Kalmar aikin ƙarfi na nufin kowanne irin aiki tuƙuru.
- Gabaɗaya dai aiki na ma'anar kowanne irin aiki dake buƙatar ƙarfi. Ana yawan cewa aikin nada wuya.
- Ma'aikaci shi ne kowanne taliki dake kowanne irin aiki.
- A turance, ana amfani da kalmar "aikin ƙarfi" kuma da nufin naƙuda. Amma a Hausa babu haka. Kalmar ciwon haihuwa naƙuda ake cewa. Wasu harsunan suna iya kasancewa da kalmomi daban daga wannan.
- Hanyoyin fassara "aikin ƙarfi" zasu iya haɗawa da "aiki" ko "aiki tuƙuru" ko "aiki mai wuya" ko "ayi aiki tuƙuru."
(Hakanan duba: tuƙuru, zafin naƙuda)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tasalonikawa 02:09
- 1 Tasalonikawa 03:05
- Galatiyawa 04:10-11
- Yakubu 05:04
- Yahaya 04:38
- Luka 10:02
- Matiyu 10:10