2.0 KiB
2.0 KiB
sani, sanin, Ilimi, sananne, bada sani, sanin gaba, Ilimin gaba
Ma'ana
"A sani" na ma'anar a fahimci wani abu ko ayi la'akari da abu zahiri. Faɗin "bada sani" faɗi ne dake ma'anar faɗar bayyana labari.
- Kalmar "ilimi" na nufin bayyana labari da mutane suka sani. Yana iya nufin sanin abubuwa a duniyoyin zahiri da na ruhaniya dukka.
- "sani game da" Allah na ma'ana fahimtar al'amura game da shi saboda abin da ya bayyana mana.
- "A san" Allah na ma'anar a kasance da zumunci tare da shi. Wannan ma ya haɗa da sanin mutane.
- A san nufin Allah na ma'anar a san abin da ya dokatar, ko a fahimci abin da Allah yake so wani taliki yayi.
- "A san shari'a" na ma'anar a faɗaka da abin da Allah ya dokatar ko a fahimci abin da Allah ya umarta a cikin shari'ar da yaba Musa.
- Wasu lokutta "ilimi" ana amfani da shi a madadin "hikima," wanda ya haɗa da yin rayuwa ta hanyar da ta gamshi Allah.
- "Sanin Allah" wasu lokutta ana amfani da shi a mamadin "tsoron Yahweh."
Shawarwarin Fassara:
- Bisa ga nassin. hanyoyin fassara "sani" zasu haɗa da "fahimta" ko "ganewa da" ko "faɗaka da" ko "sabawa da" ko "kasancewa cikin zumunci da."
- Wasu harsunan suna da kalmomi biyu daban domin "sani," ɗaya domin sanin al'amura ɗaya kuma domin sanin wani taliki da kasancewa cikin zumunta da shi.
- Kalmar "bada sani" ana iya fassarawa a matsayin "sanya mutane su sani" ko "bayyanawa" ko "faɗi game da" ko "yin bayani."
- A "sani game da" wani lokaci ana iya fassarawa a matsayin "a faɗaka da" ko "a saba da."
- Faɗar "a san yadda za'a" na ma'anar a fahimci matakai ko hanyoyin samun aiwatar da wani abu. Ana iya kuma fassarawa a matsayin "iya aiwatar da" ko "samun dabarar yin."
- Kalmar "ilimi" ana iya fassarawa a matsayin "abin da aka sani" ko "hikima" ko "fahimta," ya danganta da nassin.
(Hakanan duba: shari'a, bayyana, fahimta, wayau)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Korintiyawa 02:12-13
- 1 Sama'ila 17:46
- 2 Korintiyawa 02:15
- 2 Bitrus 01:3-4
- Maimaitawar Shari'a 04:39-40
- Farawa 19:05
- Luka 01:77