917 B
917 B
ginsi, ginsosi,
Ma'ana
Kalmar "jinsi" ko "jinsosi" suna nufin ƙungiyoyi ko rukunonin abubuwa waɗanda keda dangantaka da juna a ɗabi'arsu.
- A cikin Littafi Mai tsarki, ana amfani da wannan kalma musamman wajen bambantawa tsakanin ire-iren itatuwa da na dabbobi waɗanda Allah ya yi da ya halicci duniya.
- Yawanci akwai bambanci iri-iri a cikin kawanne "jinsi." Misali, dawakai, alfadarai, da jakuna dukkan su 'yan "jinsi" iri ɗaya ne, amma rukuni daban-daban.
- Babban abin da ya bambanta kowanne "jinsi" a matsayin ƙungiya daban shi ne 'yan waɗannan ƙungiya suna haihuwar irin "jinsinsu." 'Yan ƙungiyar rukuni daban basu iya yin haka da juna.
Shawarwarin Fassara:
- Hanyoyin fassara wannan kalma na iya haɗawa da "iri" ko "aji" ko "ƙungiya" ko "ƙungiyar itatuwa da dabba" ko "rukuni."
Wuraren da ake samunsu a Littafi Mai Tsarki:
- Farawa 01:21
- Farawa 01:24
- Markus 09:29
- Matiyu 13:47