1002 B
1002 B
alƙali, alƙalai
Ma'ana
Alƙali wani taliki ne wanda ke ɗaukar matakin menene dai-dai ko laifi sa'ad da mutane suka sami saɓani a tsakaninsu, musamman a al'amuran da suka shafi shari'a.
- A cikin Littafi Mai Tsarki, yawanci ana kiran Allah Mai shari'a ko Mai hukunci domin shine Alƙali cikakke wanda ke ɗaukar mataki na ƙarshe game da abin da ke dai-dai ko laifi.
- Bayan da mutanen Isra'ila suka shiga ƙasar Kan'ana kafin kuma su fara yin sarakunan da suka yi mulkinsu, Allah na zaɓar shugabanni da ake kira "alƙalai" su bida su a lokuttan tsanani. Yawanci waɗannan alƙalai hafsoshin sojoji ne waɗanda suka ceto Isra'ila ta wurin kayar da maƙiyansu.
- Kalmar "alƙali" ana iya kiransa kuma "mai ɗaukar mataki" ko "shugaba" ko "mai kuɓutarwa" ko "gwamna," ya danganta ga nassin.
(Hakanan duba: gwamna, alƙali, shari'a)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 2 Timoti 04:08
- Ayyukan Manzanni 07:27
- Luka 11:19
- Luka 12:14
- Luka 18:1-2
- Matiyu 05:25
- Rut 01:01