2.2 KiB
2.2 KiB
farinciki, cike da farinciki, jin daɗi
Ma'ana
Farinciki wani yanayi ne na jin daɗi a rai ko gamsuwa mai zurfi dake zuwa daga Allah. Wannan kalma "cike da farinciki" tana maganar wani taliki mai jin daɗi sosai kuma cike da murna mai zurfi.
- Wani taliki na jin farinciki sa'ad da yake cikin yanayi mai zurfi na cewa abin da yake fuskanta mai kyau ne sosai.
- Allah shine mai bayar da farinciki na gaskiya ga mutane.
- Samun farinciki baya dogara ga al'amura masu gamsarwa. Allah na iya ba mutane farinciki ko sa'ad da mawuyatan abubuwa ke faruwa a rayuwarsu.
- Wasu lokuta ana kwatanta wasu wurare a matsayin cike da farinciki, kamar su gidaje ko birane. Wannan na ma'anar cewa mutanen dake ciki suna cike da farinciki.
Kalmar "farinciki" na ma'anar cike da farinciki da murna.
- Wannan kalma yawanci na ma'anar zama cikin yanayin murna sosai game da abubuwa masu kyau da Allah yayi.
- Ana iya fassara ta a matsayin "yin murna sosai" ko "jin daɗi sosai."
- Sa'ad da Maryamu tace "raina na farinciki cikin Allah Maicetona," tana nufin "Allah Maicetona ya sani murna sosai" ko "Ina jin farinciki sosai saboda abin da Allah Maicetona yayi mani."
Shawarwarin Fassarawa:
- Kalmar "farinciki" ana iya fassara ta a matsayin "murna" ko "jin daɗi" ko "babbar murna."
- Faɗin, "yi farinciki" ana iya fassara ta a matsayin "farinciki" ko "yin murna sosai" ko ana iya fassara ta a matsayin "yin farinciki sosai cikin nagartar Allah."
- Talikin dake cike da farinciki ana iya kwatanta shi a matsayin "mai murna sosai" ko "jin daɗi" ko "murna mai zurfi."
- Faɗin kamar haka "a yi sowa ta farinciki" ana iya fassara ta a matsayin "a yi sowa ta hanyar da za a nuna murna sosai."
- "Birni cike da farinciki" ko "gida cike da farinciki" ana iya fassara ta a matsayin "birnin da mutane cike da farinciki ke zama" ko "gida cike da mutane masu farinciki."
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Nehemiya 08:10
- Zabura 048:02
- Ishaya 56:6-7
- Irmiya 15:15-16
- Matiyu 02:9-10
- Luka 15:07
- Luka 19:37-38
- Yahaya 03:29
- Ayyukan Manzanni 16:32-34
- Romawa 05:1-2
- Romawa 15:30-32
- Galatiyawa 05:23
- Filibiyawa 04:10-13
- 1 Tasalonikawa 01:6-7
- 1 Tasalonikawa 05:16
- Filimon 01:4-7
- Yakubu 01:02
- 3 Yahaya 01:1-4