943 B
943 B
nagarta
Ma'ana
Kalmar nan "nagarta" tana nufin zama da aminci, daq kuma ƙaƙƙarfan horon kai da halaiya su ake kira nagarta.
- Zama da nagarta kuma yana nufin yin zaɓi na yin abin da ke na aminci da kuma daidai koma a lokacin da ba wanda ke gani.
- Waɗansu fitattun mutane cikin Littafi Mai Tsarki, kamar Yosef da Daniyel, sun nuna nagarta a lokacin da suka ƙi su yi abin da ke mugu suka kuma zaɓi su yi biyayyya ga Allah.
- Littafin Misalai na cewa ya fi kyau a zama da talauci da kuma nagarta fiye da a zama da wadata ta wurin rashawa da rashin aminci.
Shawarwarin Fassara:
- Kalmar nan "nagarta" za'a iya fassara ta da "aminci" ko "yin rayuwar da ke dai-dai" ko "nuna halaiya ta gaskiya" ko "yin abu na aminci, rayuwa ta aminci."
(Hakanan duba: Daniyel, Yosef (Tsohon Alƙawari))
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Sarakuna 09:04
- Ayuba 02:3
- Ayuba 04:06
- Littafin Misalai 10:8-9
- Zabura 026:1-3