964 B
964 B
turaren ƙamshi na ƙonawa, turaren ƙamshi iri-iri
Ma'ana
Kalmar nan turare tana nufin gaurayayyun sinadarai masu ƙamshi da ake ƙonawa domin su bada ƙamshi mai daɗi.
- Allah yi faɗawa Isra'ilawa cewa su ƙona turare a matsayin baiko a gare shi.
- Turaren za a auna shi ne da ma'auni dai-dai bisa ga irinsa kamar dai yadda Allah ya umarta. Wanan turare ne ayyananne, don haka ba a yarda su yi aiki da shi ba barkatai.
- A ƙona turare a ƙalla sau huɗu a rana, a kowacce sa'ar addu'a. Hakanan ana ƙona shi a lokacin baiko na ƙonawa
- Ƙona turare na zama a matsayin addu'a da sujada da ake miƙawa Allah daga mutanensa.
- Sauran hanyoyi na fassara turaren wuta su ne "turaren hayaƙi" turaren ganyayyaki" ko "tsirai masu daɗin ƙamshi."
(Hakanan duba: bagadin ƙona turare, baiko na ƙonawa, turaren ƙamshi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Sarakuna 03:1-3
- 2 Tarihi 13:10-11
- 2 Sarakuna 14:04
- Fitowa 25:3-7
- Luka 01:10