1.2 KiB
1.2 KiB
siffofi na ƙarfe, alamomi, shafaffu, ƙarafa na zubi, siffofi
Ma'ana
Waɗannan kalmomin an mori dukkansu domin a ambaci gumaka domin yin sujada ga allolin ƙarya. Bisa ga tsarin bautar gumaka, kalmar "siffa" an taƙaita kalmar "gumaka ne sassaƙaƙƙu."
- "Sassaƙaƙƙiyar siffa" ko "sassaƙaƙƙiyar gumaka" kayan itace ne da aka mayar su zama kamar dabba, mutum, ko abu.
- Wannan "siffa ta zubi ta ƙarfe" siffa ce da aka narka ƙarfe aka zuba shi cikin wata kama ta dabba, ko mutum.
- Waɗannan siffofi na ƙarfe da na katako akan more su a cikin sujada ga allolin ƙarya.
- Kalmar nan "siffa" in ana magana game da gunki ko dai na katako ka na ƙarfe.
Shawarwarin Fassara:
- Lokacin da ake ambaton gunki, kalmar "siffa" za'a iya fassara ta da "gunki" ko "sassaƙaƙƙun siffofi" domin wata "hidima ta addini."
- Za'a iya gane shi a fili a waɗansu harsunan har kullum suna amfani da nuni game da wannan wajen ambaton wannan siffa a wuraren sujada.
- A tabbatar an bayyana shi a fili don aga cewa ya bambanta da mutum da aka halitta cikin kamanni Allah.
(Hakanan duba: allahn ƙarya, Allah, kamannin Allah)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Sarakuna 14:9-10
- Ayyukan Manzanni 07:43
- Ishaya 21:8-9
- Matiyu 22:21
- Romawa 01:23