822 B
822 B
doki, dawaki, dokin yaƙi, dawakan yaki, bayan doki
Ma'ana
Doki wata babbar dabba ce mai ƙafa huɗu wadda a cikin Littafi mai Tsarki ake moron ta domin aikin gona da kuma ɗaukan mutane.
- Waɗansu dawakan ana morarsu su gungura karusai, waɗansu kuma na ɗaukan mutane.
- Akan fi morar dawakai da linzami takunkumi a kansu sabo da a iya sarrafa su.
- A cikin Littafi Mai Tsarki an ɗauke su akan babubuwa ne masu daraja da kuma dukiya, mafi yawa akan amfaninsu a fagen yaƙi. Misali, wani sashe na dukiyar Sarki Suleman mai girma ita ce dubban dawakansa da karusansa da yake da su.
- Dabbobi da ke kama da doki sune jaki da alfadari.
(Hakanan duba: karusa, jaki, Suleman)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tarihi 18:04
- 2 Sarakuna 02:11
- Fitowa 14:23-25
- Ezekiyel 23:5-7
- Zakariya 06:08