858 B
858 B
nish, nishe-nishe, nisawa, yin nishi, yin nishe-nishe
Ma'ana
Kalmar nan "nishi" tana nufin yin wata 'yar ajiyarzuciya mai nauyi wadda kan samu a sakamakon wani al'amari ko dai zahirance ko kuma a cikin tunani ko kuma wata damuwa. Zai iya zama wani huci ne da wani ya fitar ba tare da waɗansu kalmomi ba.
- Mutum kan iya nisawa a sakamokon alhini da yake ji a jikinsa.
- Hakanan nisawa kan iya faruwa a sakamakon wani mummunan abin takaici ko wani hali na ƙuntatawa.
- Waɗansu hanyoyi na fassara "nishi" sun haɗa da, yin ɗan kukan zuci na wahala" ko kuma matuƙar baƙin ciki."
- A sunance, wanan zai iya zama "wani ɗan kuka ne sakamakon damuwa" ko kuma "wani babban gunaguni na wahala."
(Hakanan duba: kuka)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 2 Korintiyawa 05:2
- Ibraniyawa 13:17
- Ayuba 23:2
- Zabura 032:3-4
- Zabura 102:5-6