1.1 KiB
1.1 KiB
ɗan inabi, ya'yan inabi, garkar 'ya'yan inabi
Ma'ana
Ɗan inabi wani ɗan ƙarami, kwallon ɗan itace ne, mai kofe mai taushi kuma yakan fita ne a jikin inabi. A kan yi amfani da ruwansa domin yin ruwan inabi.
- 'Ya'yan inabi suna nan kala-kala, kamar kore-kore, mai ruwan tsanwa, ko ja
- Yadda itacen inabi yake yakan kai kamar mita uku a girma.
- Mutane kan dasa inabi a cikin lambu wanda ake kira garka. Kuma sukan zama wata babbar garka ce ta inabi.
- 'Ya'yan inabi abinci ne mai matuƙar muhimmanci a kwanaki Littafi Mai Tsarki kuma zama da garka ta inabi wanan na nuna alamar wadata.
- Domin hana 'ya'yan inabi lalacewa, mutane kan fi yawan shanya su. Busassun 'ya'yan inabi ana kiran su "kauɗar inabi" kuma ana moron su domin ayi wainar kauɗar inabi.
- Yesu ya faɗi misali game da garkar 'ya'yan inabi domin ya koyar da almajiransa game da mulkin Allah.
(Hakanan duba: inabi, garkar inabi, ruwan inabi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Maimaitawar Shari'a 23:24
- Hosiya 09:10
- Ayuba 15:33
- Luka 06:43-44
- Matiyu 07:15-17
- Matiyu 21:33