734 B
734 B
hatsi, tsabar hatsi, filayen hatsi
Ma'ana
Kalmar nan "hatsi" abin da take nufi a kullum shi ne iri amfanin gona kamar alkama, sha'ir, dawa, gero, ko shinkafa. Hakanan zai iya zama duk wani abu mai tsaba.
- A cikin Littafi Mai Tsarki, tsabar da aka fi ambato ita ce alkama da sha'ir
- Zangarniyar hatsi wani sashe ne na amfani da ke fitar da tsaba.
- A yi la'akari da cewa a Tsohuwar fassarar Littafi Mai Tsarki duk wata kalma hatsi na nufin hatsi ne kai tsaye. A sabuwar fassarar turanci shima "hatsi" na nufin tsabar wani irin hatsi ne.
(Hakanan duba: zangarniya, alkama)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Farawa 42:3
- Farawa 42:26-28
- Farawa 43:1-2
- Luka 06:2
- Markus 02:24
- Matiyu 13:7-9
- Rut 01:22