914 B
914 B
idi, idodi
Ma'ana
A bai ɗaya idi wani taro ne da mutane ko al'uma ke yi.
- Kalmar nan "idi" a cikin Tsohon Alƙawari ma'anarta ita ce wani "keɓaɓɓen lokaci"
- Idodin da Yahudawa ke yi ana yin su ne bisa keɓaɓɓun lokuta ko yanayoyin da Allah ya umarce su su yi.
- A waɗansu fassarori na turanci, akan mori kalmar "biki" a memakon "idi" sabo da bikin ya haɗa da cin abinci mai yawa tare.
- Akwai idodi da yawa da Yahudawa ke yin bikinsu a kowacce shekara:
- Idin Ƙetarewa
- Idin nunar 'ya'yan hatsi na farko
- Idin Makonni (Fentakost)
- Idin Kakaki
- Idin Kafara
- idin Bukkoki
- Dalilan yin waɗannan idodin shi ne domin a godewa Allah da kuma tunawa da ayukansa na al'ajabi da ya yi domin kariya da kuɓutarwa da kuma tanadin da ya yiwa mutanensa.
(Hakanan duba: biki)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tarihi 23:31
- 2 Tarihi 08:13
- Fitowa 05:01
- Yahaya 04:45
- Luka 22:01