902 B
902 B
baiko na zumunci, baye-baye na zumunci
Ma'ana
A cikin Tsohon Alkawari "baiko na zumunci"wata irin hadaya ce da akan bayar sabo da dalilai daban da ban, kamar yi wa Allah godiya ko kuma cika wa'adi.
- Wanan baikon na bukatar hadayar dabba da zata iya zama mace ko namiji. Wanan ta bambanta da baiko na ƙonawa, da ke bukatar dabba namiji.
- Bayan an bayar da kaso na hadayar Allah, sai shi mutumin da ya kawo hadayar zumunci ya raba naman tare da firistoci da sauran Isra'ilawa.
- Akwai abinci da ke tattare da wanan baikon wanda ya haɗa da gurasa marar yisti.
- A waɗansu lokuta ana kiran ta "baiko na salama."
(Hakanan duba: baikon ƙonawa, cikawa, baiko na hatsi, baiko na laifi, baiko na salama, firist, hadaya, gurasa marar yisti, wa'adi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tarihi 21:25-27
- 2 Tarihi 29:35
- Fitowa 24:5-6
- Lebitikus 03:3-5
- Littafin Lissafi 06:13-15