880 B
880 B
tsananin yunwa, yunwa
Ma'ana
Kalmar nan tsananin yunwa tana nufin matsanancin yanayi na ƙarancin abinci a cikin dukkan ƙasa ko wani yanki kuma yakan faru ne a sakamakon ƙarancin ruwan sama wato fãri.
- Haka nan abinci kan kasa samuwa a sakamakon ƙarancin ruwa, ko wani ciwo na amfanin gona.
- A cikin Littafi Mai Tsarki Allah kan saukar da yunwa domin ya hukunta al'uma a lokacin da suka yi zunubi.
- A cikin Amos 8:11 kalmar nan "yunwa" an yi amfani da ita ta "salon magana domin a nuna lokacin da Allah zai hukunta mutanensa ta wurin rashin yi musu magana. Za'a iya fassara wanan kalma da "yunwa" a cikin harshenku, ko kuma a irin kalmominku kamar "matsanancin ƙaranci" ko "matsanancin zalunci."
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tarihi 21:11-12
- Ayyukan Manzanni 07:11
- Farawa 12:10
- Farawa 45:6
- Irmiya 11:21-23
- Luka 04:25
- Matiyu 24:08