826 B
826 B
annabin ƙarya, annabawan ƙarya
Ma'ana
Annabin ƙarya mutum ne da ke yiƙirarin cewa soƙonsa daga Allah ne.
- Ba kasafai anabcin annabawan ƙarya ke cika ba. Wanan ya nuna cewa ba gaskiya bane anabcin nasu.
- Annabawan ƙarya kan koyar da saƙonni da ke hannun riga da abin da littafi mai tsarki ya faɗa.
- Kalmar nan za'a iya fassara ta da "mutumin da ke ƙaryar cewa shi ɗan saƙo ne na Allah" ko wani dake ƙaryar cewa yana faɗin maganar Allah ne."
- Sabon Alƙawari yana koyar da cewa a ƙarshen zamani za'a sami annabawan ƙarya da yawa waɗanda za su yi ƙoƙari su ruɗi mutane da tunanin cewa su daga Allah suke.
(Hakanan duba: cika, annabi, gaskiya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Yahaya 04:1-3
- 2 Bitrus 02:1
- Ayyukan Manzanni 13:6-8
- Luka 06:26
- Matiyu 07:16
- Matiyu 24:23-25