1.1 KiB
1.1 KiB
dattijo, dattawa, tsoho
Ma'ana
Dattawa sune waɗanda suka manyanta a ruhaniya waɗanda aka danƙawa sha'anin gudanar ayukan Ikkilisiya da kuma ayuka na ruhaniya a cikin mutanen Allah.
- Kalmar nan "dattijo" ta samo asali ne ganin cewa tun farko an san dattawa a matsayin mutane masu yawan shekaru, waɗanda sabo da shekarunsu da abubuwan da suka fuskanta suka zama da hikima.
- A cikin Tsohon Alƙawari dattawa sun temaka wajen shugabantar Isra'ilawa akan tabbatar da adalci a cikin mutane da kuma shari'ar Musa.
- A cikin Sabon Alƙawari, dattawan Yahudawa sun ci gaba da zama dattawa a cikin mutanensu, su ne kuma masu yi wa mutane shari'a.
- A farkon Ikkilisiyar Krista, dattawa su ne ke gudanar da al'amura na ruhaniya a taron masubi.
- Dattawa a waɗannan Ikkilisiyu sun haɗa da matasa waɗanda suka manyanta akan al'amura na ruhaniya.
- Za'a iya fassara kalmar a matsayin "dattawan mutane" ko mutanen da suka girma a ruhaniya da ke shugabantar ikilisiya."
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tarihi 11:1-3
- 1 Timoti 03:1-3
- 1 Timoti 04:14
- Ayyukan Manzanni 05:19-21
- Ayyukan Manzanni 14:23
- Markus 11:28
- Matiyu 21:23-24