855 B
855 B
mikiya, mikiyoyi
Ma'ana
Mikiya wata babbar tsuntsuwa ce mai iko wadda ke firiya tana cin ƙananan dabbobi, kamar kifi, ɓera, maciji da kaji.
- Littafi Mai Tsarki ya kwatanta sauri da ƙarfi na sojoji da yadda sukan kai bãra kan yadda mikiya ke kawo bãra domin ta kama abin da ta samu.
- Ishaya ya baiyana cewa waɗanda suka dogara ga Ubangiji za su yi shawagi kamar yadda mikiya ke yi. Wanan salon magana ne aka mora domin a nuna irin 'yanci da kuma ƙarfi da akan samu a cikin dogara da kuma yin biyayyya da Allah.
- A cikin Littafin Daniyel, an kwatanta tsawon sumar sarki Nebukadnezza da tsawon fiffiken mikiya wanda ya fi kamu hamsin a tsawo.
(Hakanan duba: Daniyel, 'yanci, Nebudkadnezar, iko)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 2 Sama'ila 01:23
- Daniyel 07:4
- Irmiya 04:13-15
- Lebitikus 11:13-16
- Wahayin Yahaya 04:7