930 B
930 B
ɓarna, abin da aka ɓarnatar, ɓarnatawa, aikin ɓarnatarwa, ayukan ɓarna
Ma'ana
Kalmar nan ɓarna ko ɓarnatarwa tana ma'anar a ɓarnatar da mallakar wani, ko kuma a mayar da ƙasa kufai, ko a hallakar da ita, wanan ya haɗa da karkashe da kuma kame mutanen ƙasar.
- Wanan na ma'anar mummunar ɓarnatarwa.
- Alal misali,birnin saduma an "ɓarnatar" da shi ta wurin hukuncin Allah, sabo da zunubin mutanen ƙasar
- Kalmar nan ɓarnatarwa zata iya nuna abin takaici da ƙuncin da ya biyo bayan hukuncin hallakawa.
Shawarwarin Fassara:
- Kalmar nan ɓarna za'a iya fassara ta da "hallakarwa ɗungun" ko kuma "a mai da wuri ya zama kufai ɗungun."
- Ya danganta dai da abin da wurin ke nufi, amma dai barnatarwa na nufin "ayi kaca-kaca da wuri baki ɗaya" ko kuma ya jawo "mummunan takaici" ko "masifa."
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Daniyel 08:24-25
- Irmiya 04:13
- Lissafi 21:30
- Zafaniya 01:13