1.4 KiB
1.4 KiB
ƙyama, abin da aka ƙyamata, aikin ƙyama
Ma'ana
Kalmar nan "ƙyama" tana nufin wani abu da za'a ƙi so a kuma ƙi shi. A ƙyamaci abu wannan na nufin a ƙi shi sosai.
- A lokuta da yawa Littafi mai tsarki ya yi magana akan abubuwan banƙyama na mugunta. Wanan na nufin mu ƙi mugunta mu kuma guje ta.
- Allah ya yi amfani da kalmar "aikinbanƙyama" domin baiyana miyagun ayuka na masu bautar allolin ƙarya.
- Isra'ilawa an umarce su da su "ƙyamaci" halin zunubi, muguwar ɗabi'a na waɗanda ke kewaye da su ko kuma maƙwaftaka da su ke yi.
- Allah ya kira dukkan wani nau'i na jima'i ba bisa ka'ida ba akan "aikin banƙyama".
- Duba .sihiri da miƙa yara hadaya duk ayuka ne na "banƙyama" ga Allah.
- Kalmar nan ƙyama za'a iya fassara ta da cewa "abu ne da aka ƙi sosai" ko kuma aka ɗauke shi "haramtacce na mugunta"
- Kalmar nan "aikin banƙyama" za'a iya fassarar ta akan duk wani mummunan aikin mugunta" "wanda kan sa a ƙi mutum"
- In an alaƙanta shi ga adalin mutum aikin ban ƙyama abin ƙi ne ga adalin mutum, abu ne da ya ke ƙi.
- Allah ya faɗa wa Isra'ilawa da su "ƙyamaci" waɗansu ire-iren dabbobi waɗanda Allah ya aiyana a matsayin "mara sa tsarki" ba su dace da zama abinci ba, Za'a iya fassara wanan akan babbar "ƙiyayya" ko "abin da ba'a karɓa ba."
(Hakanan duba: tsafta)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Farawa 43:32
- Irmiya 07:30
- Lebitikus 11:10
- Luka 16:15
- Wahayin Yahaya 17:3-5