1.2 KiB
1.2 KiB
datse
Ma'ana
Wannan kalma "datse" ma'anarta a ware ko raba wani da wasu mutane, a yashe da wani ko a fitar da wani can gefe daga ƙungiya. Zai kuma iya zama kisa daga mahukunci sabili da zunubi.
- A cikin Tsohon Alƙawari, rashin biyayya ga umarnan Allah yakan sa a datse mutum, ko a raba shi da mutanen Allah da kuma fuskarsa.
- Allah kuma ya ce zai "datse" ko ya hallakar da al'umman da ba Isra'ilawa ba domin basu yi masa sujada ba ko su yi masa biyayya kuma maƙiyan Isra'ila ne.
- Wannan furci "datse" an yi amfani da ita lokacin da Allah ya sa kogi ya dena gangarowa.
Shawarwarin Fassara:
- Wannan magana "datsewa" za a iya fassarata haka "a kore shi" ko "a sallame shi" ko "a raba shi da" ko "a kashe" ko "a hallaka."
- Ya danganta ga yadda aka yi amfani da shi, za a iya fassara wannan magana "a datse" ta zama "a lalatar" ko "a sallame shi" ko "a rabu da" ko "a lalatar."
- Idan ana magana game da gangarowar ruwaye da aks datse, za a iya fassara shi haka "aka tsaida su" ko "aka sa su dena gangarowa" ko "aka raba su."
- Ma'anar yanka wani abu da wuƙa zai banbamta da yadda aka yi amfani da wannan kalma "datsewa."
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Farawa 17:14
- Littafin Alƙalai 21:06
- Littafin Misalai 23:18