754 B
754 B
mai shayarwa
Ma'ana
- A lokacin Tsohon Alƙawari, "mai shayarwa baran sarki ne wanda shi ke hidimar kawo wa sarki ruwan inabi a moɗarsa, yawancin lokaci sai ya ɗanɗana da fari ya tabbatar ba a sa dafi ba.
- Ma'anar wannan a sauƙaƙe shi ne "mai kawo moɗar sha" ko "wani mutum wanda yake kawo moɗa."
- Mai shayarwa an san shi mutum ne da za a iya dogara a gareshi mai aminci ne ga sarki.
- Saboda matsayinsa na aminci, mai shayarwa yana da hannu cikin yanke shari'ar da mai mulki ke yi.
- Nehemiya mai shayarwa ne na Sarki Artashate na Fasha a lokacin da wasu Isra'ilawa suke bautar talala a Babila.
(Hakanan duba: Atazazas, Babila, bawa, Fasiya, Fir'auna)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Sarakuna 10:3-5
- Nehemiya 01:11