718 B
718 B
kuka, kwala kuka
Ma'ana
Waɗannan maganganu "kuka" ko "kwala kuka" yawancin lokaci faɗin wani abu ne da ƙara da kuma hamzari. Wani zai "kwala kuka" don ciwo ko wahala ko fushi.
- Wannan furci "kwala kuka" yana da ma'anar ihu, kira da ƙarfi, yawancin lokaci da nufin neman taimako.
- Wannan magana kuma za a iya fasara ta haka, "yin mamaki da ƙara" ko "a nemi taimako da sauri," ya danganta ga yadda zai shiga cikin rubutu.
- Magana kamar haka, "na yi kuka gare ka" za a iya fassara shi "na kira ka domin taimako" ko "na kira ka da sauri domin in roƙe ka taimako."
(Hakanan duba: kira, roƙo)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayuba 27:09
- Markus 05:5-6
- Markus 06:48-50
- Zabura 022:1-2