633 B
633 B
laifi, mai laifi
Ma'ana
Wannan kalma "laifi" ma'anar, zunubi ne da ya haɗa da karya dokar ƙasa ko lardi. Wannan kalma "mai laifi" na nufin mutumin da ya karya doka.
- Wasu irin laifufuka sune abubuwa kamar su kisan kai ko satan kayan wani.
- Yawancin lokaci akan kama mai laifi a ajiye shi kamar ɗan kamu cikin kurkuku.
- A cikin Littafi Mai Tsarki wasu masu laifi suka gudu suna yawo barkatai domin su guje wa mutanen da suke so su cuce su sakamako laifin da suka yi.
(Hakanan duba: ɓarawo)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 2 Timoti 02:09
- Hosiya 06:8-9
- Ayuba 31:26-28
- Luka 23:32
- Matiyu 27:23-24