2.1 KiB
2.1 KiB
hallita, hallitu, ma'hallici
Ma'ana
Wannan kalma "hallita" ma'anarta shi ne ayi wani abu, ko a sa wani abu ya zamo. Dukkan abin da aka hallita ana kiransu "hallitu." Akan ce da Allah "Ma'hallici" domin shi ne ya sa kome a dukkan faɗin sammai suka kasance.
- Lokacin da ake amfani da wannan kalma game da Allah daya hallici duniya, ana nufin bai yi ta da kome ba.
- Sa'ad da mutane suka "hallici" wani abu, sun yi shi ne da wani abin da ya rigaya ya kasance.
- Wani lokaci ana amfani da kalmar nan "hallita" a misalta wani abin da ba shi ganuwa, kamar a ce hallita salama ko hallita sabuwar zuciya a cikin wani mutum.
- Wannan kalma "hallitu" ya ambato tun farkon duniya ne lokacin da Allah ya hallici dukkan kome. Za a iya amfani da shi a faɗi dukkan kome da Allah ya hallita. Wani lokaci kalmar nan "hallitu" yana magana ne musamman game da mutanen duniya.
Shawarwarin Fassara:
- Wasu yaruruka za su buƙaci kai tsaye su ce Allah ya hallici duniya "ba daga wani abu ba" domin su tabbabatar sun fid da ma'anar.
- Wannan furci, "tun daga hallitar duniya" ma'anar ta, "tun lokacin da Allah ya hallici duniya."
- Wata furci mai kama da waccan ita ce, "a farkon hallitu" za a iya fasasra ta haka "lokacin da Allah ya hallici duniya a farkon lokaci" ko "lokacin da aka hallici duniya da farko."
- Yin wa'azin labari mai daɗi "ga dukkan hallitu" na nufin a yi wa'azin labari mai daɗi "ga dukkan mutane a ko'ina a doron duniya."
- Wannan furci "bari dukkan hallitu su yi farin ciki" ma'anar ta, "bari dukkan abin da Allah ya hallita su yi farin ciki."
- Ya danganta yadda za a yi amfani da shi cikin nassi, "hallita" za a iya fassara ta haka, "a yi" ko "sa abu ya zamo" ko "yin wani abu ba daga kome ba."
- Wannan kalma "Ma'hallici" za a iya fassara shi haka, "Wannan da yayi abu dukka" ko "Allah, da yayi duniya dukka."
- Furci kamar haka "Ma'hallicinka" za a iya fassara shi haka "Allahn da ya hallice ka."
(Hakanan duba: Allah, labari mai daɗi, duniya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Korintiyawa 11:9-10
- 1 Bitrus 04:17-19
- Kolosiyawa 01:15
- Galatiyawa 06:15
- Farawa 01:01
- Farawa 14:19-20